Limamin Tehran: Wajibi Ne A Bude Tattaunawa Tsakanin 'Yan Shi'a Da Gwamnatin Najeriya

Limamin Tehran: Wajibi Ne A Bude Tattaunawa Tsakanin 'Yan Shi'a Da Gwamnatin Najeriya

Wanda ya jagoranci Sallar Juma'a a Tehran Ayatullah Muwahhidi Karmani ya bayyana takaicinsa akan kisan da aka yi wa 'yan shi'a masu tattakin arba'in a Najeriya.

Limamin na Tehran ya kuma ce; Babu wani dalili da zai sa a kai hari akan tattakin da 'yan shi'ar suke yi cikin ruwan sanyi, don haka ya zama wajibi ga 'yan shi'ar da su zauna akan teburin tattaunawa da gwamnatin kasarsu domin fahimtar juna da cimma matsaya.

Bugu da kari limamin na Tehran ya ce malaman addini da maraji'ai za su iya taka rawa ta hanyar shiryarwa da kuma nasihohi domin kaucewa sake maimaita abin da ya faru.

Da ya ke magana akan tattakin da aka yi a kasashen duniya daban-daban, limamin na Tehran ya ce;sakon da ke tattare da shi, shi ne kalubalantar zalunci da danniya.

Akan alakar Amurka da Iran kuwa, limanin na Tehran ya ce lokacin nuna karfi ya zo karshe a duniya, kuma Amurka ta zama saniyar ware a duniya a wannan lokacin.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky