Limain Juma'ar Tehran Ya Bukatar Samun Hadin Kai Tsakanin Kasashen Musulmi

Limain Juma'ar Tehran Ya Bukatar Samun Hadin Kai Tsakanin Kasashen Musulmi

Limamin da ya jagoranci sallar Juma'a a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya jaddada bukatar samun hadin kai da fahimtar juna tsakanin kasashen musulmi domin kalubalantar makircin makiya.

A hudubar sallar Juma'arsa a jiya  a babban Masallacin birnin Tehran: Ayatullahi Imami Kashani ya tabo batun zaman taron shugabannin Majalisun Dokoki na kasashen musulmi na kungiyar O.I.C karo na 13 da ake gudanarwa a birnin Tehran na kasar Iran; Yama mai bayyana cewa: Manufar makiya Iran da sauran kasashen musulmi ita ce kokarin ganin sun raba su da Musulunci, sakamakon haka dole ne a kasashen musulmi su fadaka domin kalubalantar duk wani makirce-makircen da makiya ke kitsawa kansu musamman Amurka da Haramtacciyar kasar Isra'ila.

Ayatullahi Kashani ya kuma yi kakkausar suka kan shirun da wasu kasashen musulmi suka yi dangane da matsalar Palasdinu da Yamen. yana mai jaddada cewar matsalar Palasdinu tana matsayin matsalar da ta shafi farkon alkiblar musulmi ce sakamakon haka akwai bukatar nuna jarumta, ba matakin yin shiru ba.   


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky