Kyautar makudan kudi na jiran wanda ya taimaka wajen gano Shekau

Kyautar makudan kudi na jiran wanda ya taimaka wajen gano Shekau

Rundunar Sojin Najeriya ta yi shelar bada kyautar naira miliyan 3, ga duk wanda ya taimaka da bayanai wajen gano maboyar jagoran kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau

Alkawarin yana kunshe cikin sanarwar da kakakin rundunar sojin Nigeria Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka ya sa wa hannu, inda ya bukaci duka wanda ke da muhimmin bayani yana iya garzayawa hedikwatar sojoji mafi kusa ko kuma kiran wannan lamba 193.

Shelar ta zo ne kwanaki kadan, bayan da sojin Najeriyar suka ce Shekau yana kokarin tserewa daga yankin arewa maso gabashin kasar ta hanyar batar da kama da shigar mata.

Rundunar sojin Najeriyar ta ce, ta samu sahihin rahoton ne daga mayakan kungiyar ta Boko Haram da ta kama a baya bayan nan, wadan suka tabbatar da cewa jagoran nasu Shekau yana shigar mata ta hanyar sanya Hijabi baki ko kuma ruwan bula, da nufin samun nasarar tserewa, sakamakon kara kaimin farmakin sojojin Najeriya na ‘Operation Lafiya Dole’ a Sambisa.

A farkon makon watan Fabarairu, jagoran kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar da wani sabon sako na bidiyo, in da yake cewa ya gaji da masifar da suke fuskanta kuma ya gwammace mutuwarsa don hanzarta shiga aljanna.

A cikin sakon bidiyon na harshen Hausa, mai tsawon mintuna 10, Shekau ya bayyana matukar takaicinsa kan yadda ake kashe ‘yan kungiyarsa kuma ya ce, hakarsa ba ta cimma ruwa ba


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky