Kungiyoyin Kwadago Sun Yi Barazanar Sake Shiga Wani Yajin Aiki A Nageria

Kungiyoyin Kwadago Sun Yi Barazanar Sake Shiga Wani Yajin Aiki A Nageria

Gamayyar kungiyoyin kwadago a Najeriya sun yi barazanar sake shiga yajin aiki na kasa baki daya, matukar dai gwamnati ta ci gaba da yin biris da batun karin mafi karancin albashi.

Shafin yada labarai na Daily Post ya bayar da rahoton cewa, a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, gamayyar kungiyoyin kwadagon na Najeriya, da suka hada da NLC, TUC, da kuma ULC, sun gargadi gwamnatin tarayya da cewa, za su tsunduma a cikin yajin aiki na sai baba-ta-gani, matukar dai gwamnati ta ci gaba da yin biris da bukatar da suka gabatar mata kan batun karin albashi.

Bayanin ya ce gwamnati tana da lokaci daga nan zuwa ranar 6 ga watan Nuwamba mai kamawa, domin ta kawo karshen wannan matsala ta hanyar sauraren wannan bukata da suka gabatar, idan kuma ba haka ba, to kuwa za su shiga yajin aiki na kasa baki daya.

Haka nan kuma kungiyoyin kwadagon sun yi Allawadai da matakin da gwanati ta sanar, kan cewa babu albashi ga duk wani ma'aikaci da ya tafi yajin aiki, tare da jaddada cewa hakan ba zai taba tsorata su ba.

Gwamnatin Najeriya dai ta gabatar da tayin biyan albashi Naira dubu 24 a matsayin albashi mafi karanci ga ma'aikaci a kasar, maimakon Naira dubu 55 da kungiyoyin kwadago suka gabatar, amma tuni kungiyoyin kwadagon suka yi watsi da wannan tayi na gwamnati.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky