Kungiyar 'Yan Ta'addan ISIS Ta Tabbatar Da Mutuwar Bagdadi

Kungiyar 'Yan Ta'addan ISIS Ta Tabbatar Da Mutuwar Bagdadi

Cikin Sanarwar da fitar, Kungiyar Ta'adancin Ta ISIS ta tabbatar da mutuwar Shugaban ta Abubakar Bagdadi

Kafar watsa Labaran Sumarit News ta kasar Iraki ta habarta cewa a wannan Talata Kungiyar ta'addanci ta ISIS ta fitar da wani kajeran labari inda a cikin sa ta tabbatar da mutuwar Shugabanta Abubakar Bagadadi tare da cewa nan gaba za ta sanar da sabon Khalifanta.

Kafar watsa labaran ta ce kwanaki biyu da suka gabata, cikin wani sako da fitar a shafinta na Intagram kungiyar ta ISIS ta haramta watsa duk wani labari da ya shafi mutuwar Shugaban Kungiyar Abubakar Bagdadi, domin hakan ne ma masu sharhi ke ganin cewa wannan shi ne dalilin da ya sanya kungiyar ta ISIS ta gaggauta tabbatar da mutuwar ta Bagdadi.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky