Kungiyar IS tana kira ga magoya bayanta a fadin duniya da su fadada hare hare a watan azumi.

Kungiyar IS tana kira ga magoya bayanta a fadin duniya da su fadada hare hare a  watan azumi.

Kungiyar 'yan ta'adda ta IS tana kira ga magoya bayanta a duk fadin duniya su kai hare hare a wannan watan mai tsarki na azumi.

Wani da yake kiran kansa kakakin kungiyar ne ya yi wannan kiran a shafin sandarwar internet na kungiyar ta 'yan ta'adda ISIS da ake kira Telegram.

Kasashen da suke shirin kaiwa harin sun hada da Amurka, da Rasha da Australia da Iran da Iraq da Syria da Philipins, da kuma kasashen Turai.

Kungiyar 'yan ta'addan ta IS ta dauki alhakin tagwayen hare haren da aka kai a Tehran wanda yai sanadiyar shahadar mutane goma sha bakwai. Kakakin ya yi kira da a kara kai hare haren bom a Iran, da cewa, yanar gizo tafi kasar karfi.

Kungiyar 'yan ta'addan IS ta saba kira ga magoya bayanta su kai hare hare lokacin azumi, da aka fara ranar ishirin da shida ga watan Mayu, da za a kuma gama ranar ishirin da hudu ga watan Yuni.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky