Kungiyar Hamsa Ta Gargadi HKI A Dai-Dai Lokacinda Take Kara Kuntatawa Mutanen Yankin Gaza

Kungiyar Hamsa Ta Gargadi HKI A Dai-Dai Lokacinda Take Kara Kuntatawa Mutanen Yankin Gaza

Kungiyar Hamasa mai gwagwarmaya da HKI da makamai ta gargadi HKI kan matakan da take dauka na rufe hanyoyin shigar makamashi da abinci zuwa yankin Gaza.

Tashar talabijin ta Presstv a nan tehran ta bayyana cewa a ranar 9 ga watan Yuli da muke ciki ne HKI ta rufe kofar shiga yankin Gaza ta Keren Shalon ga kayakin bukatun yau da kulum zuwa yan na Gaza a abinda ta bayyana na cewa "Murkushe kungiyar Hasar". HKI ta bayyana cewa zata ci gaba da rufe wannan mashigar matukan Palasdinawa sun ci gaba da aiko takardun dauke da makamashi ta iska zuwa yankunan da yahudawa suke zaune. 

A wani labarin kuma a dai dai lokacinda HKI ta rufe mashigar yankin Gaza ta Kerem Shalon gwamnatin kasar Masar ma ta rufe mashiga Rafa zuwa yankin Gazar ta tare da bayyana dalilin yin  haka ba. 

Banda haka yahudawa sun hana Palasdinawan kamun kifi daga nisan kilomita na ruwa 6 zuwa 3 kacal don takurawa mutanen yankin na gaza.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky