Kungiyar Hamas Ta Halba Rokoki 220 Zuwa Yankunan Yahudawa

Kungiyar Hamas Ta Halba Rokoki 220 Zuwa Yankunan Yahudawa

Dakarun Gwagwarmayar Palastiwa sun mayar da martani kan hare-haren da jiragen yakin Sahayuna suka yankin zirin gaza, daga daren jiya laraba zuwa wayewar yau alhamis, sun halba rokoki akalla 220 zuwa yankunan yahudawa 'yan kama wuri zauna dake kudancin Palastinu.

Kungiyar gwagwarmayar Palastinawa ta Hamas ta sanar da halba rokoki akalla 220 zuwa yankunan yahudawa 'yan kama wuri zauna dake kudancin palastinu daga daren jiya laraba zuwa safiyar yau alhamis, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar sojojin sahayuwa 11 da kuma sanya tsoro a zukatan yahudawan, inda suka nemi mafuka a cibiyoyin agaji.

Kungiyar ta Hamas ta ce ta halba rokokin ne a sansanin sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma kauyukan yahudawa 'yan kama wuri zauna dake kan iyaka da yankin zirin gaza a matsayin mayar da martani.

A bangare guda, a wannan Alhamis jiragen yakin Haramtacciyar kasar Isra'ila sun sake kai hare-hare a yankunan Arratisi na arewa maso yammaci da yarmuk gami da Askalan dake kudancin yankin zirin Gaza.

A ranaikun talata da laraba da suka gabata, jiragen yakin sahayunan sun ruwan bama-bamai a yankin zirin gaza, lamarin da ya yi sanadiyar shahadar Palastinawa uku da kuma jikkata wasu da dama na daban.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky