Kungiyar Fateh al-Cham Ta Dauki Alhakjin Kai Harin Damascos

Kungiyar Fateh al-Cham Ta Dauki Alhakjin Kai Harin Damascos

Kungiyar Fateh al-Cham wace ta kasance tsohon reshen Al'Qaida a kasar Syria ta ce ita ce keda alhakain kai munanen hare haren da sukayi sanadin mutuwar mutane da dama a birnin Damascus na kasar Syria.

Kamfanin dilancin labaren faransa na AFP ya rawaito wata sanarwa da kungiyar mai da'awar jihadi da na cewa wasu gwarzayenta biyu ne suka kai harin na jiya Asabar.

Kawo yanzu mutane 74 ne aka tabbatar da mutuwarsu a jerin hare haren da aka kai mabiya mazahbar shi'a galibi 'yan asalin kasar Iraki dake ziyara a wani tsohon gari dake Damascus.

Wannan dai shi ne hari mafi muni da aka kai a Damascos babban birnin kasar ta Syria a cikin shekaru shida na yakin basasa da kasar ke fama da shi.

Tunda farko dai wasu alkaluma da hukumar dake sa ido kan kare hakkin bil adama ta kasa a Syria (OSDH) ta fitar sun ce akalla mutane 59 ne suka ras arayukansu da suka hada da 'yan shi'a 47 da kuma wasu jami'an tsaro Syria 12 da kuma wasu da dama da suka raunana ciki har da masu munanen raunuka.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky