Kungiyar Boko Haram Ta Saki Wasu Karin 'Yan Matan Chibok 82 Da Ta Yi Garkuwa Da Su

Kungiyar Boko Haram Ta Saki Wasu Karin 'Yan Matan Chibok 82 Da Ta Yi Garkuwa Da Su

Majiyar fadar shugaban Nigeriya ta sanar da cewa: Mayakan kungiyar Boko Haram sun saki wasu karin 'yan matan Chibok 82 da suka yi garkuwa da su tun a shekara ta 2014.

Gidan talabijin na Aljazeera na kasar Qatar ya watsa rahoton cewa: Majiyar fadar shugaban Nigeriya ta sanar da cerwa 'yan kungiyar Boko Haram sun saki wasu daga cikin 'yan matan Chibok da yawansu ya kai 82 da suka yi garkuwa da su tun a watan Aprilun shekara ta 2014 a jiya Asabar da a halin yanzu haka 'yan matan suke garin Banki da ke kan iyaka da Jamhuriyar Kamaru.

Rahoton ya kara da cewa: Sakin 'yan matan ya zo ne bayan wata musayar fursunoni da aka yi tsakanin gwamnatin Nigeriya da kungiyar ta Boko Haram karkashin shiga tsakanin gwamnatin Switzerland da kungiyar bada agajin gaggawa ta Red Cross gami da wasu kungiyoyin da suke ciki da wajen Nigeriya.

Ana sa-ran a yau Lahadi za a kwashi 'yan matan na Chibok zuwa birnin Abuja fadar mulkin Nigeriya domin ganawa da shugaban kasar Muhammadu Bukhari.

Tun a ranar 14 ga watan Aprilun shekara ta 2014 ne mayakan kungiyar Boko Haram suka kai farmaki makarantar sakandari na 'yan mata da ke garin Chibok a jihar Borno da ke shiyar arewa maso gabashin Nigeriya, inda suka yi awungaba da dalibai 'yan mata 276 amma jami'an tsaron kasar sun samu nasarar 'yanto wasu daga cikinsu, kamar yadda wasu adadi masu yawa na 'yan matan suka samu nasarar tserewa daga hannun 'yan kungiyar ta Boko Haram.  


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky