Kungiyar Boko Haram Ta Kame 'Wasu Yan Sanda Mata A Maiduguri

Kungiyar Boko Haram Ta Kame 'Wasu Yan Sanda Mata A Maiduguri

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar da wani sabon Bidiyo ta kafofin sadarwa na zamani, in da yayi ikirarin cewa a halin yanzu sun yi garkuwa da wasu jami'an 'yan sanda mata da suka kama a hanyar Maiduguri zuwa Damboa da ke jihar Borno na Najeriya.

Sakon bidiyon na tsawon minti 16 ya nuna Abubakar Shekau ba cikin kuzari ba kuma bai faye motsa barin jikinsa ba, kamar yadda ya yi a hotunan bidiyon da ya fitar a can baya ba,Shekau ya ce, jami'an 'yan sanda matan na hannunsu a matsayin bayi, ya kuma bayyana malaman addinin Islama a Najeriya a matsayin masu ci da Al-Kur’ani, yayin da ya ce, malaman sun manta da mahaliccinsu.

Shekau ya kuma bayyana sarakunan gargajiya na Najeriya a matsayin makaryata da ke yaudarar jama'arsu.

Kazalika mayakan na Boko Haram sun kira kansu a matsayin musulmi na asali.

A wani labarin da ake da alaka da ta'addancin Boko haram,Hukumomi a Najeriya sun fara aikin zagaye Jami'ar Maiduguri da ramuka don kare makarantar daga hare-haren kungiyar Boko Haram.

Sanarwar fara aikin wanda zai kai nisan kilomita 27 kuma zai ci naira miliyan 50, ta zo ne kwana guda bayan wasu 'yan kunar bakin wake sun kai hari jami'ar, inda suka kashe kansu da kuma wata ma'aikaciya.

A ranar Litinin ne Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya sanar da aikin fara gina ramukan, yayin da ya kai ziyara jami'ar don duba ta'adin da maharan suka yi.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky