Kenya : 'Yan Adawa Sun Yi Watsi Da Sakamakon Zabe

Kenya : 'Yan Adawa Sun Yi Watsi Da Sakamakon Zabe

'Yan adawa a Kenya sun yi watsi da sakamakon wucin gadi na zaben shugaban kasar dake nuna shugaba mai barin gado Uhuru Kenyatta kan gaba.

Sakamakon zaben dai ya nuna cewa Uhuru Kenyatta na kan gaba da kashi sama da 55% a kri'un da aka kada a zaben na jiya, inda ya baiwa abokin hamayarsa Raila Odinga tazara ta kusan kuri'u miliyan daya da rabi.

Mista Odinga wanda sakamakon ya ce ya samu kashi kusan 45%, ya bayyana a wani taron manema labarai a cikin daren jiya cewa alkalumen zaben na bogi ne.

Kafin hakan dai bayanai daga kasar sun ce zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali a mafi yawan wurare, a inda ita kuwa hukumar zaben kasar ta yi kira ga jama'ar kasar su kai zuciya nesa su jira sakamakon zaben cikin kwaciyar hankali.

Jama'a dai a kasar na da fargabar sake barkewar rikicin bayan zabe irin wanda aka yi a shekara ta 2007 wanda ya yi ajalin mutane 1'100 tare kuma da cilastawa wasu 600,000 barin muhallansu.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky