Kasashe 122 Sun Amince Da Kudirin Haramta Makaman Nukiliya A Duniya

Kasashe 122 Sun Amince Da Kudirin Haramta Makaman Nukiliya A Duniya

A zaman babban zauren majalisar dinkin duniya da aka gudanar a jiya, kasashe 122 ne suka amince da kudirin da ke haramta makaman nukiliya, ci gaba da kera su, ko inganta su da kuma barazanar yin amfani da su.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a yayin gudanar da zaman, dukkanin kasashe 9 da ke mallakar makaman nukiliya, wato Amurka, Rasha, China, Birtaniya, Faransa, India, Pakistan, Koriya ta arewa da kuma Isra'ila ba su halarci zaman ba, kamar yadda da dama daga cikin kasashe mambobi na NATO sun kaurace ma zaman, da hakan ya hada har da Japan wadda Amurka ta yi amfani da wadannan makamai a kanta a shekara ta 1945 ta kaurace ma zaman.

Bayan amincewa da wannan kudiri, kasashen Amurka, Birtaniya da kuma Faransa sun sanar da cewa ba za su taba amincewa da wannan kudiri ba, saboda bai yi la'akari da barazanar da wasu ke yi kan amfani da wadannan makamai ba.

Sai dai mafi kasashen duniya da suka hada da Switzerland, Sweeden, Iran, Brazil, Masar, Afirka ta kudu, Mexico, Austria da sauransu, sun amince da wannan kudiri, da kuma wajabcin yin aiki da abin da ya kunsa.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky