KasarSaudiyya Na Bukatar Koyon Bayan Amruka Don Ci Gaba Da Kai Hari A Kasar Yaman

KasarSaudiyya Na Bukatar Koyon Bayan Amruka Don Ci Gaba Da Kai Hari A Kasar Yaman

Kawancin kasar Saudia wadanda suke yakar kasar Yemen sun bukaci taimakon Amurka don kwace iko da birnin Hudaida na bakin ruwa a kasar ta Yemen.

Tashar talabijin ta Rasha Today ta nakalto wasu jami'an gwamnatin Amurka wadanda suke da masaniya kan lamarin suna cewa Hadaddiyar daular Larabawa ta gabatar da bukata kai tsaye, a madadin kawancen ga sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo inda take neman taimko don kwace garin Hudaida na bakin ruwa a kasar Yeman.

Labarin ya kara da cewa kawancen kasashen larabawan suna ganin mayakan huthi suna amfani da tashar jiragen ruwa na Hudaida don shigo da makamai kasar. Sai dai kungoyoyin bada agaji suna ganin duk wani kokari na kwace birnin daga hannun mayakan Huthi zai jefa rayukan mutane kimani 400,000 dake cikin cikin hatsari.

Kawancen dai a wannan karon tana bukatar Amurka ta bada taimakon leken asiri da jiragenta masu leken asiri a shirinsu na kwace birnin na Hudaida.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky