Kasar Saudiyya Ta Zargi Iran A Kan Taimakawa Yemen

Kasar Saudiyya Ta Zargi Iran A Kan Taimakawa Yemen

Mahukuntan Saudiyya sun gabatar da koke a gaban kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran

A ci gaba da zargin da mahukuntan Saudiyya suke yi na cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ce ke aikewa da makamai ga al'ummar Yamen, mahukuntan na Saudiyya sun gabatar da koke a gaban kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya cewa: Makami mai linzami da sojojin Yamen da hadin gwiwar dakarun sa-kai na kungiyar Ansarullahi ta kasar suka harba kan kasar ta Saudiyya kirar kasar Iran ne.

Jakadan kasar Saudiyya a Majlisar Dinkin Duniya Abdullahi Al-Mu'ulami ne ya gabatar da takardar koken ga kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya, kuma koken yana dauke da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ci gaba da aikewa da makamai masu linzami ga sojojin na Yamen.

Manufar mahukuntan Saudiyya ita ce kokarin ganin manyan kasashen duniya sun sake yin ca kan kasar Iran, kamar yadda a watannin baya jakadiyar Amurka a Majalisar ta Dinkin Duniya ta gabatar da irin wannan zargi kan kasar ta Iran.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky