Kasar Iran Ta Musanta Kashe Wasu Dakarunta A Yayin Fada Da Wasu 'Yan Ta'adda

Kasar Iran Ta Musanta Kashe Wasu Dakarunta A Yayin Fada Da Wasu 'Yan Ta'adda

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran sun musanta labarin da wasu kafafen watsa labarai masu adawa da juyin juya halin Musuluncin suke yadawa na kashe wani adadi na dakarun yayin wani gumurzu da suka yi da wasu gungun 'yan ta'adda a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labaran kasar Iran (IRNA) ya bayyana cewar dakarun kare juyin juya halin Musuluncin sun bayyana hakan ne cikini wata sanarwa da ofishin hulda da jama'a na sansanin Hamza shugaban shahidai (a.s) na sojin kasa na dakarun kare juyin Musuluncin ya fitar inda yace a yayin gumurzun da dakarun sansanin suka yi da wasu kungiyoyi uku na 'yan ta'addan a yankun Sarvabad da Oshnavieh da ke arewa maso gabashin kasar ta Iran, dakarun sun sami nasarar kashe 'yan ta'adda 13 da kuma raunana wasu da dama.

Har ila yau sanarwar ta kara da cewa dukkanin dakarun kare juyin da suka kasance a wajen wannan gumurzun suna nan cikin koshin lafiyansu, sabanin abin da kafafen watsa labarai da suke da alaka da kungiyoyin 'yan ta'addan da kuma ma'abota girman kan duniya suke yadawa da nufin kashe gwiwan dakarun da kuma al'ummar Iran. Don haka sanarwar ta ce irin wadannan farfagandar koda wasa ba za ta yi wani tasiri cikin azamar da dakarun suke da ita na kare kasar Iran da kuma fada da duk wata barazana da za ta iya fuskanta ba.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky