Kasar Amurka Tana Son Sake Raba Kasar Sudan

Kasar Amurka Tana Son Sake Raba Kasar Sudan

Shugaban kasar Sudan ya bayyana cewa: Kasar Amurka tana kokarin ganin ta sake raba kasar Sudan ce zuwa kasashen biyar.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Associated Press a lokacin ziyarar aikin da ya kai zuwa kasar Rasha: Shugaban kasar Sudan Umar Hasan Albashir ya yi furuci da cewar sun samu rahoton sirri cewa gwamnatin Amurka tana kokarin ganin ta sake raba kasar Sudan zuwa kananan kasashe biyar.

Shugaban kasar ta Sudan ya kara da cewa: Kasashen yammain Turai musamman Amurka suna kokarin ganin ta kowace hanya sun raunana karfin sojin Sudan da matakan tsaron kasar, don haka suke kokarin ganin sun raba kasar zuwa kananan kasashe biyar.

A karshe shugaba Umar Hasan Albashir ya bayyana fatan ganin kasar Rasha ta dauki matakin goyon bayan Sudan domin tsare ta daga tsoma bakin kasar Amurka da nufin ci gaba da kasancewar Sudan kasar daya dunkulalliya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky