Kare Hakkin Bil'adama Na Kasashen Yamma Ba Gaskiya Ba Ne

Kare Hakkin Bil'adama Na Kasashen Yamma Ba Gaskiya Ba Ne

Limamin da ya jagoranci sallar Jumma'a a nan Tehran Hujjul Islam Kazeem Sadiqi ya bayyana cewa ikrarir kare hakkin bil'adama wanda kasashen yamma suke yi ba na gaskiya bane.

Majiyar muryar JMI ta nakalto Hujjatul Islam Sadiqi yana cewa, idan gaskiya ne wadan nan kasashen suna son kare hakkin bil'adama, ta ya ya suka yi gum da bakunansu kan irin ta'asar da gwamnatocin kasashen Saudia da Bahrai suke aikatawa a cikin kasashensu da kuma, kasar Yeman.

Limamin har'ila yau ya yi kira ga gwamnatin Nigeria ta kawo karshen tsare shugaban kungiyar harka Islamia ta Nigeria Sheikh Ibrahim Zakazaky, wanda take tsare da shi fiye da shekara guda ba tare da bayyana dalilan tsare shi ba. 

A wani bangare na khudubarsa Limamin ya yi ishara kan yadda gwamnatin kasar Azarbajan take hana musulman kasar hatta karatun Al-qur'ani mai girma dakuma gudanar da tarurrukan addini.

A ranar litinin da ta gabata ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Aya. Aliyul Khaminaee, a lokacinda yake ganawa da jami'an ma'aikatar sharia'ar kasar ya bukaci ma'aikatar ta shiga cikin lamuran musulman sauran kasashen duniya, musamman wadanda ake zalunta don bayyana matsayinta dangane da su.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky