Jumhuriyar Musulunci Ta Iran Zata Ci Gaba Da Aikace Aikacenta Na Tace Makamashin Uranium

Jumhuriyar Musulunci Ta Iran Zata Ci Gaba Da Aikace Aikacenta Na Tace Makamashin Uranium

Hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran ta bada sanarwan cewa zata dawo da aikin tace makamashin Uranium bisa sharruddan yerjejeniyar 2015 tare da manya manyan kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto kakakin hukumar nukliya ta kasar Iran Behrouz Kamalvandi yana fadar haka a jiya Litinin, jim kadan bayan da jagoran juyin juya halin musulunci Aya. Sayyid Aliyul Khamana'i ya bayyana cewa za'a dawo da aikin tashe uranium a kasar.

Kamalvandi ya kara da cewa gwamnatin Iran zata mikawa hukumar IAEA mai kula da harkokin makamashin nukliya ta duniya wasika dongane da hakan daga ofishin jakadancinta da ke Venna .

A cikin jawabinsa na jiya a munasamar wafatin Imam Kkomaini (q) wanda ya assasa JMI, Aya. Khaminae jagoran juyin juya halin musulunci ya bayyana cewa Iran ba zata ci gaba da mutuntuta yerjejeniyar Nukliya ta 2015 sannan kuma a gefe guda ana ci gaba da dora mata takunkumai kamar yadda wasu kasashe su ke zata ba.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky