Jami'an Tsaron Iran Sun Tarwatsa Kungiyar Munafukan Ta MKO A Kasar

Jami'an Tsaron Iran Sun Tarwatsa Kungiyar Munafukan Ta MKO A Kasar

Jami'an tsaron kasar Iran sun sanar da tarwatsa wata kungiyar ta 'yan kungiyar munafukai ta kasar da aka fi sani da MKO wacce ta taka gagarumar rawa cikin rikicin baya-bayan nan da ya faru a kasar ta Iran.

Kafafen watsa labarai sun jiyo cibiyar jami'an tsaron na lardin Lorestan tana cewa jami'an tsaron lardin sun sami nasarar nasarar gano 'yan wannan kungiya ta ta'addanci da suke da alaka da kungiyar munafukan ta  Mujahedin-e Khalq Organization (MKO) a garin Borujerd, a jiya Juma'a inda suka kama su gaba daya bayan wani gumurzu.

Har ila yau Ma'aikatar tsaron cikin gida na  Iran din ta sanar da tarwatsa wata kungiyar ta'addancin a lardin Azarbaijan ta Yamma da ke arewa maso yammacin kasar ta Iran wadanda su ma suke cikin kai wasu hare-hare a kasar.

Sakamakon wasu 'yan rikice-rikice da suka faru a kasar ta Iran biyo bayan wasu zanga-zangogin da mutanen wasu garuruwa suka yi don nuna rashin amincewarsu da tashin farashin kayayyaki, wasu kasashen waje sun yi amfani da irin wadannan kungiyoyi na ta'addanci don haifar da rikici da hare-hare a kasar ta Iran don cimma bakar aniyarsu.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky