Jakadun Kasashen Afirka 54 A MDD Sun Fitar Da Bayanin Yin Tir Da Donald Trump

Jakadun Kasashen Afirka 54 A MDD Sun Fitar Da Bayanin Yin Tir Da Donald Trump

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato cewa; Jakadun na kasashen Afirka sun fitar da bayani ne wanda kuma ya kunshi kira ga shugaban na Amurka da ya janye abinda ya furta, ya kuma nemi gafara

Jakadun na kasashen Afirka sun kuma cigaba da nuna damuwarsu akan nunawa Amurkawa yan asalin Afirka wariya a cikin Amurka, hakan nan kuma 'yan gudun hijira bakakan fata.

A ranar alhamis din da ta gabata ne dai shugabn kasar ta Amurka Donald Trump ya bayyana kasashen Haiti, El-savardor da kasashen nahiyar Afirka da cewa kazanta ne. Haka nan kuma ya bukaci da a daina karbar yan gudun hijira daga wadannan kasashen.

Kasar Haiti ta kira yi jakadan Amurka zuwa ma'aikatar harkokin waje domin nuna kin amincewa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky