Jagoran Juyin Musulunci Na Iran Kai Hari Kan Kasar Syria Laifi Ne

 Jagoran Juyin Musulunci Na Iran Kai Hari Kan Kasar Syria Laifi Ne

Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei ya bayyana harin da Amurka da Birtaniya gami da Faransa suka kaddamar kan Syria a da jijjifin safiyar jiya a matsayin babban laifi, kuma ma'abota girman kai tabbas daga karshe za su sha kayi.

Jagoran ya bayyana hakan ne a jiya lokacin da yake ganawa da wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin kasar Iran, da kuma wasu daga cikin jakadun kasashen musulmi, gami da wasu daga cikin al'umma da suka halarci wurin, inda ya bayyana shugabannin kasashen Amurka, Birtaniya da Faransa da cewa masu laifi ne.

Ya ce Amurka kamar yadda ba ta ci ribar komai ba a Afghanistan da Iraki, ba za ta taba cin wata riba  akan kasar Syria ba.

Jagoran ya kara da cewa; babbar manufar Amurka ba ita ce rusa Afghanistan ko Iraki ko kuma Syria ba, babbar manufar ita ce karya lagon al'ummar musulmi, saboda haka ya zama wajibi kasashen musulmi su zama cikin fadaka, domin kada su fada cikin masu yin hidima ga Amurka domin cimma wannan manufa ta rusa al'ummar musulmi.

A yayin da yake yin ishara da shigar Iran a cikin kasar Syria, bayan kasancewar hakan ya zo ne bisa bukatar gwamnatin kasar ta Syria, Iran tana burin ganin ta taimaka ma duk wata al'umma da ake zalunta, saboda haka Iran tana taimaka ma sojojin Syria masu jarunta wajen fuskantar makircin makiya al'umma, inda suka samu nasarar karya lagon 'yan ta'adda, wadanda Amurka da saudiyya da wasu kasashen yammacin turai suke daukar nauyinsu a Syria.

Haka nan kuma ya jinjinawa tsayin dakan da al'ummar Palastine suke yi wajen kin mika wuya ga bakaken manufofin haramtacciyar kasar Isra'ila na zalunci da danniya, inda ya ce duk da irin matsin da al'ummar Palastine ke ciki, amma sakamakon tsayin daka da jajircewar da suke yi a gaban haramtacciyar gwamnatin yahudawa, sun zama al'umma mai girma da jarunta a duniya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky