Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Ya Jinjinawa Jami'an Hukumar Tsaron Farar Kaya Ta Kasar

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Ya Jinjinawa Jami'an Hukumar Tsaron Farar Kaya Ta Kasar

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada bukatar ganin ayyukan hukumar tsaron farar kaya ta kasar ya hada dukkanin bangarori da nufin rusa makirce-makircen makiya kan kasar Iran.

A ganawarsa da manyan jami'an hukumar tsaron farar kaya ta kasar Iran karkashin shugabancin Brigadier Janar Gholamreza Jalali a yau Lahadi: Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khameine'i ya jaddada muhimmancin hukumar tsaron farar kaya da irin gagarumar rawar da zata taka a fagen kalubalantar duk wata barazanar makiya kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Ayatullahi Sayyid Khameine'i ya bayyana cewa: Dole ne jami'an hukumar tsaron farar kaya su kasance cikin fadaka da shirin ko- ta kwana domin tunkarar makirce-makircen makiya tare da wargaza su.

Har ila yau Jagoran juyin juya halin na Musulunci ya jaddada yin kira ga mahukuntan kasar Iran kan fahimtar muhimmancin hukumar tsaron farar kaya ta Iran yana mai fayyace cewa: Rashin fahimtar hukumar yadda ya dace, hakan zai iya wurga kasar cikin matsalar barazana da shawo kan matsalar zai wahalar kwarai da gaske, don haka akwai bukatar dukkanin bangarorin kasar kama daga mahukunta da al'ummar Iran su dauki matakan gudanar da taimakekkeniya tsakaninsu da hukumar tsaron farar kaya ta kasar. 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky