Jagora:Duk Wurin Da Aka Bukaci Taimakon Iran Wajen Yaki Da Girman Kai Zamu Taimaka.

Jagora:Duk Wurin Da Aka Bukaci Taimakon Iran Wajen Yaki Da Girman Kai Zamu Taimaka.

Jagoran jiyun juya halin musulinci ya tabbatar da cewa: jumhoriyar musulinci ta iran ta tsaya tsayin daka kuma za ta ci gaba da tsayawa wajen tunkarar makircin girman kai da harmcecciyar kasar Iran na samar da yaki tare da sanya sabani a tsakanin al'ummar musulmi, da yardar Ubangiji kuma za ta ci nasara a wannan yaki.

A yayin ganarwa da mahalarta taron masoya iyalan gidan Anabta tsarkaka da kuma batun masu akidar kafirta mutane a safiyar yau Alkhamis, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce duk da cewa an kusa kawo karshen ta'addancin kungiyar IS a kasashen Iraki da Siriya, amma kadda mu gafala da makircin makiya saboda Amurka da HKI gami da kawayensu ba za su taba daina kiyayya da musulinci ba, kuma mai yiyuwa su sake kula wani makirci wajen samar da wata kungiya irin ta IS a wani yankin.

Jagoran juyin juya halin Musulunci  ya ce a yau duniyar musulinci na bayan gaskiya guda ne fada da kafirci gami da girman kai, tsarin musulinci a nan iran kuma na bayan tabbatar da shari'ar musulinci ne wanda hakan ita ce hanya daya cilo  na cin nasara a kan makiyan musulinci a duniya.

A yayin da yake ishara kan kimanin shekaru 40 da makiya suka kwashe suna kula makirci a kan tsarin musulinci ta hanyar sanya takunkumi da matsin lamba, jagora ya ce duk da  matsin lambar makiya, a hakikanin gaskiya ina bayyana muku cewa jumhoriyar musulinci ta Iran a duk inda ake kalubalantar kafirci da girman kai, idan akwai bukatar taimako, za mu taimaka, kuma a game a wannan maudu'i ba za mu saurari ko wani mutum ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei  ya ce maganar Palastinu ita ce mas'alar farko ga duniyar musulinci , mabudin cin nasara a kan makiyan musulinci shi ne maganar Palastinu saboda manufar makiya na samar da rashin tsaro da kuma sanya sabani a kasashen musulinci shi ne mance maganar Palastinu, tare da tabbatar da cewa ranar da kasar Palastinu za ta koma ga al'ummar Palastinu, ita ce ranar da gadan bayan makiya zai karye kuma  ita babbar rana ta cin nasarar al'ummar musulinci, domin tabbatuwar hakan za mu iya namu kokari.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky