Jagora Ya Taya Al'umma Murnar Shiga Sabuwar Shekarar Hijira Shamsiyya Ta 1397

Jagora Ya Taya Al'umma Murnar Shiga Sabuwar Shekarar Hijira Shamsiyya Ta 1397

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya taya dukkanin al'ummar Iran murnar shiga sabuwar shekarar hijira shamsiyya ta 1397 tare da jaddada muhimmancin dogaro da irin kayayyakin da ake samarwa a cikin kasar

A jawabin da ya gabatar dangane da shiga sabuwar shekarar hijira shamsiyya ta 1397 a yammacin talata: Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khamene'i ya taya dukkanin al'ummar Iran murnar shiga sabuwar shekara ta 1397 musamman iyalan shahidai, wadanda suka samu raunuka a gwagwarmayar kare kasa da kuma matasa: Yana mai karfafa gwiwar matasa kan kara himma a fagen bunkasa ci gaban kasa musamman harkar ilimi.

Har ila yau a cikin jawabinsa: Jagoran juyin juya halin na Musulunci ya tabo wasu daga cikin abubuwan da suka faru a kasar Iran na murna da kuma bakin ciki a shekarar da ta gabata ta 1396, inda ya jinjinawa al'ummar Iran kan irin gagarumar rawar da suka taka a fagen ciyar da kasarsu gaba musamman fitowa zabuka da suka yi domin bai wa marada kunya, gudanar da zanga-zangar ranar Qudus da na tunawa da ranar samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran.

Jagoran juyin juya halin na Musulunci ya kuma yi kyakkyawar fata ga al'ummar Iran kan shiga sabuwar shekarar ta 1397 cikin alheri da albarka, zaman lafiya da kwanciyar hankali. Kamar yadda ya radawa sabuwar shekarar sunan "Shekarar goyon bayan kayayyakin da ake samarwa a cikin kasa".


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky