Jagora Ya Bukaci Jami'an Iran Da Su Kara Hanzarta Kai Dauki Ga Wadanda Girgizar Kasa Ta Shafa

Jagora Ya Bukaci  Jami'an Iran Da Su Kara Hanzarta Kai Dauki Ga Wadanda Girgizar Kasa Ta Shafa

Jaoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana alhininsa dangane da girgizar kasar da ta auku a daren jiya a yankin Kermanshah da ke yammacin kasar, tare da yin kira da a kara mayar da hankali wajen kai dauki ga wadanda abin ya shafa.

A cikin sakon da jagoran ya aike da shi a safiyar yau, jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah Saiid Ali Khamenei, ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, yahna mai rokon Allah da ya yi rahma ga dukkanin wadanda suka rasu, tare da jajantawa wadanda suka samu raunuka tare da yi musu fatan Allah ya ba su lafiya.

Haka nan kuma jagora ya kirayi dukkanin bangarori na gwamnati da su bayar da agaji a cikin gaggawa ga wadanda lamarin ya shafa, inda ya ce lamarin bai takaitu ga hukumomin kai daukin gagawa ba kawai, lamari ne da ke bukatar kai gudunmawa daga dukkanin bangarori na al'umma.

Haka nan kuma ya jadda cewa sojoji gami da dakarun kare juyin juya hali da ojojin sa kai na Basij, su hanzarta kai kansu a yankunan da wannan girgizar kasa ta auku, domin taimaka ma jama'a.

Ga sauran mutanen yankunan da abin ya shafa kuwa, jagoran ya kirayi wadanda lamarin bai shafe su ba da su taimaka ma sauran 'yan uwansu da suka rasa gidajensu, kafin kammala aikin samar da wuraren zaunar da su.

Jami'an bayar da gajin gaggawa a Iran sun cewa adadin Mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasar da ta auku a yammacin kasar, ya karu zuwa 328, yayin da a Iraki kuma mahukunta sun ce mutane 8 ne suka rasu.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky