Jagora: Iran Bazata Tattauna Da Amruka Ba

Jagora: Iran Bazata Tattauna Da Amruka Ba

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Aya. Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa har yanzun idan kasar Iran ta ga ba zata cimma bukatunta a yerjejeniyar Nukliyar da ta cimma da kasashen yamma ba to zata fice.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto jagoran yana fadara haka a jiya Laraba a lokacin ganawarsa da shugaban kasa da kuma majalisar ministoci da manya manyan jami'an gwamnatin kasar a gidansa.

Jagoran ya kara da cewa akwai manufar da Iran take da shi a yerjejeniyar shirinta na makamashin nukliya ta shiga da manya manyan kasashen duniya, don haka a duk lokacinda ta ga cewa ba zata cimma wannan manufar zata yi watsi da ita.

A wani bangaren na jawabinsa Jagoran ya bukaci gwamnati ta hada kai da majalisar dokoki da kuma ma'aikatar shari'a da sauran ma'aikatu don ganin an warware matsalar tattalin arzikin da kasar take fama da ita.

Banda haka jagoran ya ce kada a dogari da abinda kasashen turai zasu yi a warware matsalolin da kasar take ciki, a ko yauce a nemi wata hanya ta warware matsaloli ba tare da su ba.

Kafin jawabin jagoran shugaban kasa Dr Hassan Ruhani ya gabatar da irin ci gaban da gwamnatinsa ta sami a cikin shekaru 5 da suka gabata.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky