Jagora: Gwagwarmaya Ita Ce Hanyar Kwato Kasar Palastinu

Jagora: Gwagwarmaya Ita Ce Hanyar Kwato Kasar Palastinu

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya sake jaddada tsohuwar siyasar kasar Iran ta goyon bayan al'ummar Palastinu a kokarin su na 'yanto kasarsu daga mamayan yahudawa yana mai bayyana cewar hanya guda daya kawai ta magance matsalar Palastinu ita ce gwagwarmaya.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne cikin amsar wasikar da shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas, Isma'il Haniya ya aiko masa kwanakin baya inda ya ce hanyar magance matsalar Palastinu ita ce karfafa bangaren gwagwarmaya da tsayin da aka a duniyar musulmi da kuma kara kaimin gwagwarmayar da fito na fito da yahudawan sahyoniya da masu daure musu baya.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Duk wani hankoron shiga tattaunawa da azzalumar gwamnatin sahyoniyawa babbar kuskure ne wanda ke jinkirta nasarar da al'ummar Palastinu za su samu a kan sahyoniyawa, don haka ko shakka babu gwagwarmaya da tsayin daka ita ce kawai hanyar tabbatar wa al'ummar Palastinu da hakkokinsu.

Jgoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Wajibi ne al'ummomi musamman matasan kasashen musulmi da na larabawa da kuma gwamnatocin da suka damu da lamarin Palastinu su sauke wannan gagarumin nauyi da ke wuyansu na fada da ma'abota girman kai da tilasta wa makiya ja da baya.

A kwanakin baya ne shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas, Isma'il Haniya ya aike wa Ayatullah Khamenei wasika yana mai bayyana masa irin gagarumin makircin da ma'abota girman kai da wasu shugabanni suke yi wa lamarin Palastinu da kuma masallacin Kudus, yana mai jinjinawa irin goyon bayan da Jagoran juyin juya halin da kuma al'ummar Iran suke ba wa al'ummar Palastinu.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky