Jagora: Batun Mai Da Qudus Helkwatar Isra'ila Wata Gazawa Ce

Jagora: Batun Mai Da Qudus Helkwatar Isra'ila Wata Gazawa Ce

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar kokarin da Amurka ta ke yi na mayar da birnin Qudus a matsayin helkwatar haramtacciyar kasar Isra'ila wata gazawa ce daga bangarensu don kuwa matsalar Palastinu wani lamari ne da ya fi karfinsu, yana mai jaddada cewar ko shakka babu za a 'yanto kasar Palastinu daga mamayar sahyoniyawa.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a yau din nan Laraba a wata ganawa da yayi da manyan jami'an kasar Iran da kuma baki mahalarta taron Makon Hadin Kai na kasa da kasa da aka gudanar a nan Tehran don tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah (s) da jikansa Imam Sadiq (a.s) inda ya ce makiyan dai babu wani abin da za su iya don kuwa lamarin Palastinu ya riga da ya fice daga hannunsu.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa siyasar Amurka a yankin Gabas ta tsakiya ita ce haifar da fitina da yake-yake don tabbatar da tsaro da zaman lafiyar haramtacciyar kasar Isra'ila, to sai dai abin bakin cikin shi ne a halin yanzu ana samun wasu shugabanni da 'yan siyasa da suke taimakon Amurka wajen cimma wannan manufa nata.

Jagora Imam Khamenei dai yana mayar da martani da kalaman shugaban Amurka Donald Trump wanda a jiya ya sanar da shugaban Palastinawa Mahmood Abbas aniyarsa ta mayar da ofishin jakadancin Amurka da haramtacciyar kasar Israilan zuwa birnin Qudus daga Tel Aviv lamarin da ke ci gaba da fuskantar tofin Allah


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky