Iran Za Ta Ci Gaba Da Mara Baya Ga Al'ummar Palastine

Iran Za Ta Ci Gaba Da Mara Baya Ga Al'ummar Palastine

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, ko da wasa Iran ba za ta taba ja fa baya ba a wajen bayar da gudnmawa da taimako ga al'ummar Palastine.

Zarif ya bayyana hakan ne a wata zantawa da ta hada shi ta wayar tarho da shugaban kungiyar hamas Isma'ila Haniyya, inda ya jaddada cewa, mara baya ga al'ummar Palastinu da kuma taimaka musu wani babban jigo ne a cikin manufofin siyasar kasar Iran.

Ya kara da cewa, lamarin Palastine lamari ne da ya shafi dukkanin al'ummar musulmi da ma duk wani dan adam mai lamiri a cikin zuciyarsa, kuma yin watsi da wannan batu na a matsayin gazawa daga dukkanin musulmi, da kuma kasashen da suke da'awar bin dimukradiyya da kare hakkokin bil adama.

A nasa bangaren Ismail Haniyya shugaban kungiyar Hamas ya jinjina wa kasar Iran dangane da irin goyon bayan da ya ce ta baiwa al'ummar palastinu a dukkanin bangarori.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky