Iran Za Ta Ci Gaba Da Kasancewa Tare Da Al'ummar Palastinu

Iran Za Ta Ci Gaba Da Kasancewa Tare Da Al'ummar Palastinu

Babban Saktaren taron kasa da kasa na goyon bayan gwagwarmayar Palastinawa ya ce har zuwa lokacin da za a 'yanto birnin Qudus, jamhoriyar musulinci ta Iran za ta ci gaba da bawa Al'umma da kungiyoyin gwagwamarya na Palastinu goyon baya.

A cikin wani sako da ya aikewa sabon shugaban kungiyar gwagwarmayar Jihadu-Islami ta Palastinu Ziyad Nakhala a jiya Asabar, babban saktaren taron kasa da kasa na goyon bayan al'ummar Palastinu kuma mataimaki na musaman ga shugaban Majalisar musulinci na kasar Iran Husain Amir Abdu ilahiyan ya tabbatar da cewa ayyukan da kungiyoyin gwagwarmaya gami da jihadin shugabanin kungiyar Jihadul-islam ke yi ba dare da bara ya bayar da gudumuwa mai yawa wajen tilastawa 'yan sahayoniya ja baya ga manufifoninsu na mamaye yankin Palastinawa.

Amir Abdu ilahiyan  har ila ya taya Ziyad Nakhala murya kan zabensa da aka yi a matsayin sabon shugaban kungiyar gwagwarmaya na Jihadu-Islami. sannan kuma ya yi wa al'ummar Palastinu da mujahidai na kungiyoyin gwagwarmayar fatan samun nasara a kan makiyansu.

A zaben da bangaren siyasa na kungiyar gwagwarmayar Palastinawa ya yi a zabi Ziyad Nakhal a matsayin sabon shugaban Kungiyar yayin da kuma aka zabi Ramadan Abdullah Shallah a matsayin mataimakinsa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky