Iran :Ta Zamu Magance Matsalar Tashin Farashin Kayayyaki

 Iran :Ta Zamu  Magance Matsalar Tashin Farashin Kayayyaki

Gwamnatin Iran Ta Sha Alwashin Magance Matsalar Tashin Farashin Kayayyaki

Gwamnatin kasar Iran ta tabbatar wa al'ummar kasar cewa za ta ci gaba da aiki tukuru wajen magance matsalar tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki da ake fuskanta a kasar lamarin da ya haifar da wasu 'yan zanga-zanga a wasu garuruwa na kasar cikin 'yan kwanakin nan inda mutane suke nuna rashin amincewarsu da wannan yanayin.

Mataimakin shugaban kasar Iran din Es’haq Jahangiri ne ya bayyana hakan yayin da yake magana dangane da irin kokarin da gwamnatin take yi a bangaren tattalin arziki duk da cewa 'yan wasu matsaloli da gazawa da ake fuskanta.

Mr. Jihangiri ya kara da cewa tashin farashin kayayyakin da aka samu din hakan ta faru ne sakamakon wasu dalilai inda ya ce gwamnatin a shirye take ta sake dubi cikin wadannan dalilai don magance su.

Ita ma a nata bangaren, majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran din ta bayyana aniyarta na dubi cikin irin matsalolin da al'umma suke fuskanta da nufin magance su cikin gaggawa tana mai bayyana cewar al'ummar Iran ba za su taba bari makiya su yi amfani da wannan lamari wajen cimma bakaken aniyarsu kan Iran din ba.

A ranar Alhamis din da ta gabata ce wasu gungun mutane a garin Mashad suka fito kan titi don nuna rashin jin dadinsu da yadda ake samun tashin gwauron zabi na farashin kayayyaki a Iran da suke dora alhakin hakan ga tsare-tsaren tattalin arziki na gwamnatin kasar, lamarin da ya watsu zuwa wasu garuruwa na kasar. 

Zanga-zangogin dai sun zo ne a daidai lokacin da wasu miliyoyin al'ummar kasar kuma suka fito don nuna goyon baya ga gwamnatin Musulunci ta kasar don tunawa da ranar 9 Dey da al'ummar kasar suka fito don nuna goyon bayansu ta tsarin musulunci na Iran bayan zaben shugaban kasa na 2009


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky