Iran Ta Musanta Batun Shawagin Wasu Jiragen 'Isra'ila' A Sararin Samaniyar Kasar

Iran Ta Musanta Batun Shawagin Wasu Jiragen 'Isra'ila' A Sararin Samaniyar Kasar

Kwamandan sansanin kare sararin samaniyya na Khatamul Anbiya (s) na sojojin Iran Birgediya Janar Farzad Esmaili yayi watsi da jita jitan da wasu kafafen watsa labarai suke watsawa na cewa an ga wasu jiragen yakin makiya suna shawagi a sararin samaniyyar Iran, yana mai cewa su ma makiyan ba za su fara hakan ba.

Kamfanin dillancin labaran Iran (IRNA) ya ce Janar Esmailin yana mayar da martani ga wasu labarai da wasu kafafen watsa labaran kasashen waje suke yadawa na cewa wasu jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila samfurin F35 sun gudanar da wasu shawagi a sararin samaniyyar kasar Iran.

Birgediya Janar Farzad Esmaili ya ce: Matukar dai gigi ya debi makiyan suka turo jiragen samansu kusa da sararin samaniyar Iran, ko shakka babu za su debi kashinsu daga wajen makaman kariya na Iran, don haka babu gaskiya cikin wannan labarin.

Kwamandan sansanin kare sararin samaniyya na Khatamul Anbiya (s) na sojojin Iran din ya ci gaba da cewa a shekarar da ta gabata, dakarun nasa sun gudanar da gagarumin aiki a duk fadin kasar Iran da nufin kare sararin samaniyyar kasar wanda kuma za a ci gaba da yin hakan don tabbatar da cikakken tsaro a kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky