Iran Ta Mayar Da Martani Kan Jawabin Bayan Taron Kasashen Larabawa Da Ya Gudana A Masar

Iran Ta Mayar Da Martani Kan Jawabin Bayan Taron  Kasashen Larabawa Da Ya Gudana A Masar

Kakakin ma'akatar harkokin wajen kasar Iran ya mayar da martani ga jawabin bayan taro na ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa karo na 146 a birnin Alkahira na kasar Masar a jiya Laraba.

Kamfanin dillancin Labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Bahram Qasimi yana cewa maganganu marasa kan gado wanda wadansu kasashen yankin gabas ta tsakiya suke yi basa taimakawa kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya da tsaron yankin.

Qasimi ya kara da cewa jawaban wakilan kasashen Kuwait da kuma Emmirate dangane da tsibiran kasar Iran na Abu-Musa Tumbe-Kuchek da Tumbe Bozarg ya nuna cewa akwai wata manufa ta siyasa a cikin zantuttukan kuma akwai alamun basu san hakikanin yadda lamarin wadan nan tsibiran suke. 

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya kara da cewa bijiro da irin wadan nan maganganu a cikin halin da ake ciki a yankin, kokari ne na kauda hankulan mutane daga muhimman lamuran da yakamata a sa a gaba. 

Ya kuma kara jaddada cewa tsarin JMI na zamantakewa da makobtan kasashe shi ne mutunta juna da kuma rashin shishigi a cikin lamuran cikin gida na wasu kasashe.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky