Iran Ta Kore Duk Wata Yiyuwar Tattaunawa Da Amurka Kan Sabuwar Yarjejeniyar Nukiliya

Iran Ta Kore Duk Wata Yiyuwar Tattaunawa Da Amurka Kan Sabuwar Yarjejeniyar Nukiliya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kore duk wata yiyuwar sake zama teburin tattaunawa da Amurka kan wata sabuwar yarjejeniyar nukiliya, tana mai kiran gwamnatin Amurkan da ta nesanci irin maganganu na batanci da barazana da take yi wa al'ummar Iran.

Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran Bahram Qassemi ne ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump a yayin ganawar da yayi da firayi ministan kasar Japan Shinzo Abe inda ya ce Amurka za ta ci gaba da kakabawa Iran takunkumin da ba a taba sanya mata ba a daidai lokacin da kuma take fatan za ta sake cimma wata yarjejeniya da Iran.

Qassemi ya ce al'ummar Iran ba su taba sauya matsaya ta adalci da suka dauka ba dangane da fada da duk wata barazanar da take fuskantarsu kuma a nan gaba ma ba za su sauya ba, don haka Iran ba za ta taba sake zama teburin tattaunawa da Amurka kan wannan batu na nukiliya ba.

Har ila yau kakakin Ma'aikatar harkokin wajen na Iran ya kara da cewa ba wai ma kan batun nukiliya ba hatta ma a sauran batutuwa na daban, Iran ba za ta zauna teburin tattaunawa da Amurka ba matukar dai ta ci gaba da yi mata barazana maimakon amfani da kalmomi na girmamawa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky