Iran Ta Ja Hankalin Amurka Kan Ta Dauki Darasi Kan Kurakurenta

Iran Ta Ja Hankalin Amurka Kan Ta Dauki Darasi Kan Kurakurenta

Bahram Qasemi kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar muslunci ta Iran ya mayar da martani a kan kalaman da Trump ya yi dangane da Iran a ziyarar da ya kai birnin Paris.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Bahram Qasemi ya bayyana kalaman da Trump ya yi a kan Iran a lokacin ziyararsa a Paris da cewa Trump ya kara tabbatar da cewa ba shi da masu ba shi shawara da suka san siyasa.

Qasemi ya ce Iran ce ta fara yaki da ayyukan ta’addanci a yankin gabas ta tsakiya, domin kuwa tun daga lokacin samun nasarar juyin Islama kasar take fuskantar ayyukan ta’addanci.

Ya kara da cewa, zargin Iran da taimaka wa ‘yan ta’adda a yankin gabas ta tsakiya da Trump ya yi a bin ban dariya ne ga duk wanda ya ji hakan, domin kuwa Iran ita ce kasar da ta zama karfen kafa ga ‘yan ta’adda a yankin da kuma kasashen da suka kirkiro su, duk kuwa da irin goyon bayan da Amurka take baiwa wadannan kasashe saboda maslharta ta siyasa da tattalin arziki.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky