Iran Ta Harba Tauraron Dan'adam Zuwa Sararin Samaniya

Iran Ta Harba Tauraron Dan'adam Zuwa Sararin Samaniya

Kwararru a nan Iran sun harba wani sabon tauraron dan'adan na watsa labarai a sararin samaniya a ranar Alhamis da ta gabata.

Tauraron mai suna Simurg yana da nauyin kilograme 250 kuma an cilla shi ne daga cibiyar harkokin sararin samaniya na Imam Khomaini da ke lardin simnan a tsakiyar kasar ta Iran. Tauraron simurga tuni ya fara aiki a tazarar kilomita 500 daga doron kasar kamar yadda aka tsara.

Tuni dai kasashen Amurka da turai suna nuna rashin amincewarsu da wannan cigaban da kasar Iran ta samu inda Amurka take cewa hakan ya sabawa kudurin majalisar dinkin duniya ta 2231 wanda ya hana Iran kera makamai masu linzami.

Amma ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zarif ya bayyana cewa aikin cilla tauraron dan adam bai sabawa kuduri na 2231 ba, don abinda kudurin ya hana iran shi ne kera makamai masu linzami wadanda suke iya daukar makaman nukliya, Zarif ya kara da cewa makamai masu linzami wadanda iran take kerawa ba mai daukar makaman nukliya bane. Ya kuma kammala da cewa Iran ba zata nemi izinin wata kasa don kare kanta ko kuma kawo ci gaban ilminta ta. 

Banda kasar Amurka gwamnatocin wasu kasashen Turai wadanda suka hada da Britani, Faransa da Jamus duk sun yi Allah wadai da cilla tauraron dan'adam wanda kasar Iran.

Shugaban komitin tsaro a majalisar dokokin kasar Iran alaiddeen Burujardi ya bayyana cewa wannan ba shi ne tauraron dan adam wanda kasar Iran ta fara cillawa ba kuma zata ci gaba da aikin kera su kamar yadda ta tsara. 288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky