Iran Na Shirin Aikewa Da Tallafi Ga Musulmin Rohingya

Iran Na Shirin Aikewa Da Tallafi Ga Musulmin Rohingya

Kungiyar agaji ta red-Crescent a Iran ta ce tana shirin aikewa da kayan tallafin abunci ga musulmin Rohingya da suka tserewa cin zarafin da jami'an tsaron Myammar ke yi masu

Tallafin dai ya kunshi kayan abunci da na bukatar yau da kulun wanda tuni aka shirya aikesu zuwa kasar ta Birma kamar shugaban hukumar Morteza Salimi ya sanar.

kamfanin dilancin labaren ISNA na kasar ta Iran wanda ya rawaito labarin ya ce tallafin za'a aike shi ne har zuwa kasar ta Myamar idan aka samu izinin hakan, wannan kuwa bisa umurnin shugaban kasar Hassan Rohani.

A cewar MDD, sama da 'yan musulmin Rohingya 160,000 ne suka yi gudun hijira zuwa kasar Bangaladash.

Dama kafin hakan jakadan kasar Iran a MDD, Gholam Ali Khoshrou ya samu tattaunawa da wasu kasashen musulmi kan yadda za'a tattauna batun 'yan Rohingya a zauren MDD.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky