Iran : Matakin Hana Baki Shiga Amurka, ''Abun Kunya Ne''

Iran : Matakin Hana Baki Shiga Amurka, ''Abun Kunya Ne''

Ministan harkokin wajen Iran, Mohammad Javad Zarif ya bayyana matakin shugaba Donal Trump kan hana baki daga kasashe shida galibi na musulmi shiga Amurka, da abun ''kunya

A cikin daren jiya ne dai wani bangare na dokar da aka dade ana ta kai kawo gaban kotunan na Amurka ta fara aiki.

Matakin wanda gwamnatin Trump ta bayyana dana hana 'yan ta'adda shiga kasar, ya tanadi haramtawa musulmin kasashen da suka hada da Iran din da Siriya, Libiya, Yemen, da Sudan da Somaliya da kuma Yemen sanya kafa cikin Amurkar har na tsawan kwanaki 90 mudun dai basu da ‘yan uwa na kud-da-kud a cen din.

Haka kuma su ma 'yan gudun hijira daga ko ina a duniya, dokar ta haramta masu shiga Amurka har na tsawan kwanaki 120.

Kafin hakan dai dubban Iraniyawa ta hanyar shaffin Twetter sun yi ta aika sakon tir da dokar, suna masu cewa kakaninsu basu da wata alaka da ta'addanci.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky