Iran : Jagora Ya Kaiwa Al'ummar Da Girgizar Kasa Ta Shafa Ziyara

Iran : Jagora Ya Kaiwa Al'ummar Da Girgizar Kasa Ta Shafa Ziyara

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya ziyarci wadanda iftila'in girgizar kasa ya shafa a yankunan Kermanshah.

Jagoran wanda ya isa a yankin da safiyar yau Litinin, ya soma da ziyartar wuraren da girgizar kasar ta yi barna a birnin Sarpol-e-Zahab, kafin daga bisani ya ziyarci iyalan wadanda suka rasa 'yan uwansu a girgizar kasar data aukawa yankin a cikin daren ranar Lahadin makon da ya gabata.

Jagoran ya kuma tattauna da iyalan akan matsaloli da kuma damuwarsu.

Yagoran ya ce yana taya su bakin ciki, kuma shi ma yana ji a jikinsa abunda suke ji a cikin irin wannan yanayi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya kuma yi addu'a ta samun sauki ga wadanda suka ji raunuka, ya ce lalle ya so ganawa da su amma ba a cikin irin wannan yanayi ba.

A hannu daya kuma jagoran ya bayyana cewa ina tare da ku a lokacin da tsohuwar gwamnatin Iraki ta mamaye wannan yankin, inda kuka nuna juriya, to ina son ku nuna mani haka sakamakon wannan iftila'in.

Girgizar kasar mai karfin maki 7.3 data aukawa yankin na Kermanshah a ranar 11 ga watan nan ta dai yi sanadin mutuwar mutane kimanin 436 da raunana wasu dubbai.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky