Iran: Hukumar Leken Asiri Ta Sanar Da Kame Masu Tayar Da Hatsaniya

Iran: Hukumar Leken Asiri Ta Sanar Da Kame Masu Tayar Da Hatsaniya

A yau litinin ne hukumar leken asirin ta Iran ta ce ma'aikatanta da kuma yan kasa sun gano da kame wadanda suke da hannu a tayar da hatsaniya akan titunan wasu biranen kasar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa a halin da ake cikin, jami'an leken asiri suna ci gaba da bin sawun wasu daga cikin masu tayar da hargitsin.

Wani sashe na sanarwar hukumar leken asirin ya ce: "Kamar yadda yan kasa suka sani, an gudanar da taruka na neman hakkoki, sai dai masu tayar da rikici sauya tarukan zuwa ta hargitsi.

Hukumar leken asirin ta kuma jinjinawa 'yan kasa nagari da suka nesanta kawukansu daga masu tada fitina, tare kuma da yin kira da dukkanin bangarorin al;'ummar kasar da su cigaba da zama cikin fadaka.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky