Iran Ba Za Ta Taba Yin Sakaci Da Tsaron Kasarta Ba

Iran Ba Za Ta Taba Yin Sakaci Da Tsaron Kasarta Ba

Kakakin Ma'aikatar harkokin waje na kasar Iran, Bahram Qassemi, ya bayyana cewar: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba yin wasa da kuma yin sakaci da tsaron kasarta ba.

Kamfanin dillancin labaran Hukumar Gidan Radio da Talabijin na Iran ya bayyana cewar Bahram Qassemin, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambaya dangane da harin da dakarun kasar Iran suka kai sansanonin 'yan ta'adda da ke cikin kasar Iraki inda ya ce: Koda wasa kai irin wadannan harin ba wai fata ne da Iran take da shi ba, to amma hare-haren da 'yan ta'adda suke kawo mata musamman harin da suka kai da yayi sanadiyyar shahadar wasu dakarun kare kan iyaka na Iran shi ne ya sanya dakarun kasar mayar da irin wannan kakkausar martanin.

A saboda haka ne kakakin Ma'aikatar harkokin wajen na Iran ya ce koda wasa Jamhuriyar Musulunci ba za ta taba yin sakaci da kuma wasa da duk wani abin da zai kasance barazana ga tsaro da zaman lafiyar al'ummarta ba.

A ranar Asabar din da ta gabata ce Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran din, cikin wata sanarwa da suka fitar, suka ce sun kai wasu hare-hare da makamai masu linzamin kan wani taro na shugabannin wata kungiyar ta'addanci da kuma wani sansani na horonsu da ke arewacin kasar Iraki da yayi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin wadannan 'yan ta'adda. Sanarwar ta kara da cewa harin yana a matsayin mayar da martani ne ga harin da 'yan ta'addan suka kai wa dakarun kare kan iyakan Iran din a kwanakin baya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky