Iran: Amurka Ba Za Ta Yi Nasara Ba A Sabon Makircin Da Take Kullawa

Iran: Amurka Ba Za Ta Yi Nasara Ba A Sabon Makircin Da Take Kullawa

Shugaban Kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya bayyana cewa; Duk da cewa Amurka ta kakabawa Iran takunkumi, kasashen duniya da dama a shriye suke su ci gaba da aiki da ita.

Shugaban kasar ta Iran ya kara da cewa kasashe da dama na duniya suna tuntubar Iran tare da bayyana cewa a shirye suke su yi aiki da ita ta fuskar tattalin arziki, abin da yake nuni da koma bayan takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran.

Dr. Hassan Rauhani ya kuma ce; Abin da Amurka take son cimmawa shi ne yin matsin lamba da takurawa da za su fusata al'ummar Iran, sai dai abin da Amurkan ba ta sani ba shi ne cewa al'ummar Iran din suna cikin fushi da ita.

Shugaban kasar jamhuriyar musulunci ta Iran din ya kuma ce; A cikin sauki za mu fice daga cikin matsalar da muke fuskanta ta hanyar ci gaba da harkokin kasuwanci da bangarori daban-daban na duniya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky