Iran A Shirye Take Ta Taimakama Kungiyoyin Palastinawa

 Iran A Shirye Take Ta Taimakama Kungiyoyin Palastinawa

Babban kwamandan dakarun Qudus na Jamhuriyar Musulunci Ta Iran (IRGC) ya bayyana cewa rundunarsa a shirye take ta tallafawa kungiyoyi masu gwagwarmaya da yahudawan Sahyoniya a Palasdinu.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto babban kwamandan Janar Kasim Sulaimani yana fadar haka a jiya litinin bayan tattaunawarsa da kwamandojin dakarun Izzuddin Qassam reshen soja na kungiyar Hamas da kuma Quds brigades na jihadul Islami ta wayar tarho. 

Janar Sulaimani ya kara jaddada wa kungiyoyin cewa dakarun Quds a shirye suke su kare masallacin Qudus ta hanyar taimakawa dakarun Palasdinawa da suke gwagwarmaya da yahudawa a halin yanzu a cikin Palasdinu da aka mamaye. 

Daga karshen Janar Sulaimani ya kammala da cewa tallafin da rundunarsa zata bawa Palasdinawan ya hada dukkan bangarorin da suke bukata.

Tun lokacin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya shelanta birnin Qdus a matsayin cibiyar gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra'ila a ranar Laraba da ta gabata ne Palasdiawan suka fara fafatawa da jami'an tsaron yahudawan Sahyonia


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky