Igbo sun dakatar da komaia yankin kudu don goyon bayan Biafra

Igbo sun dakatar da komaia yankin kudu don goyon bayan Biafra

Rahotanni daga Kudu maso Gabashin Najeriya sun ce an rufe shaguna a garuruwa da dama yayin da 'yan aware ke tunawa da ranar zagayowar kafa kasar Biafra.

Rahotanni sun ce tituna sun kasance fayau kuma an rufe kasuwanni da bankunan sai dai 'yan sanda da sojoji suna sintiri .

Al'amarin ya fi tasiri a garuruwan Nnewi da Onitsha da Aba da kuma Umuhia.

Kungiyar IPOB ta umarci mazauna yankin a kan su zauna a gida kuma rahotanni sun ce jama'a sun amsa kiran kungiyar.A shekarar 1967 'yan awaren suka bayyana ballewa daga Najeriya, sai dai lamarin ya yi sanadin barkewar yakin basasa inda fiye da mutum miliyan daya suka rasa rayukansu.

A baya baya nan an sake samun wasu 'yan yankin da ke fafitukar balewar Biafra karkashin jagorancin kungiyar IPOB, sai dai gwamnatin Najeriya ta bayyana kungiyar a matsayin ta 'yan ta'adda.

Hukumomi a Najeriya sun gargadi 'yan a waren kan kada su yi zanga zangar a ranar Laraba.A halin yanzu madugun kungiyar, Nnamdi Kanu yana fuskantar tuhumar cin amanar kasa a Najeriya.

Duk da cewa daga bisani kotu ta ba da belinsa a watan Afrilun shekarar 2017, amma hukumomin kasar na tuhumarsa da gudanar da wasu ayyuka da suka saba wa ka'idojin belinsa.

Kungiyar IPOB na fafitukar balewa daga Najeriya ne saboda a cewarsu wariyar da suka ce ana nuna wa kabilar Igbo wadda tana daya daga cikin manyan kabilun Najeriya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky