HKI Tana Kokarin Gamsar Da Kasar Saudia Kan Tafiyar Aikin Hajji Daga Birnin Telaviv

HKI Tana Kokarin Gamsar Da Kasar Saudia Kan Tafiyar Aikin Hajji Daga Birnin Telaviv

Kamfanin dillancin Labaran "Bloomberg" na kasar Amurka ya nakalto wani jami'in gwamnatin HKI yana cewa kasarsa tana kokarin gamsar da hukumomin saudia na su amince da kwasar mahajjata Palasdinawa musulmi daga tashar jiragen sama ta Bengario a birnin Telaviv zuwa birnin jidda don aikin hajjin bana.

Kafin haka dai  Mahajjata Palasdinawa su kan shiga motocin safa-safa ne zuwa kasar Saudia don saukar da Farali, tafiya wanda ya kai tsawon kilomita 1000 daga kasar ta Palasdinu.

"Bloomberg" ya nakalto ministan sadarwa na HKI Ayyub Qira yana cewa idan gwamnatin kasar saudia ta amince a bana mahajjata Palasdinawa a yankunan shekara ta 1948 zasu je aikin hajji da jiragen HKI daga tashar jiragen sama na Bengerio.

A zahiri dai kasar saudia bata da huldal diblomasia da HKI , amma tun hawan Donal Trump kan kujerar shugabancin kasar Amurka ya fara kokarin samarda huldan jakadanci tsakanin kasashen biyu.

A shekara ta 2002 gwamnatin kasar saudia ta bukaci HKI ta janye daga yankunan Palasdinawa da ta mamaye a shekara ta 1967, sannan ta amince da kafa kasar Palasdinu mai babban birnin a birnin Qudus inda ita kuma zata samar cikekken huldan jakadanci da haramtacciyar kasar, har da safarar jiragen sama tsakanin kasashen biyu. Amma gwamnatin HKI ta ki amincewa da hakan. 288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky