Hizbullah: Manufar ISIS Ita Ce Bakanta Fuskar Musulunci A Idon Duniya

Hizbullah: Manufar ISIS Ita Ce Bakanta Fuskar Musulunci A Idon Duniya

Kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon ta yi tir da Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai birnin Barcelona na kasar Spain, tare da bayyana hakan a matsayin hankoron bata sunan addinin muslunci

A cikin bayanin da kungiyar ta Hizbullah ta fitar a jiya, ta bayyana cewa ‘yan ta’addan ISIS suna ta hankoron ganin sun bata wa musulunci suna a idon duniya, tare da bata ma’anar jihadi wanda yake a matsayin aikin ibada mai girma a cikin addinin musulunci.

Kungiya Hizbullah ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin na Barcelona, tare da yin fatan samun sauki ga wadanda suka samu raunuka sakamkon harin.

A wani bangaren bayanin, kungiyar ta bukaci bangarori na kasa da kasa da su hada karfi da karfe domin tunkarar wannan babbar barazana ta ta’addancin takfiriyya, tare da taka wa masu daukar nauyin ta’addanci birki a gabas ta tsakiya da ma a wasu kasashen na duniya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky