Harin Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Mutane 13 A Maiduguri

Harin Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Mutane 13 A Maiduguri

Kimanin mutane 13 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 65 suka jikkata sanadiyar harin kunar bakin wake da aka kai Maiduguri babban birnin jahar Borno dake shiyar arewa maso gabashin Najeriya.

Wasu 'yan kunar bakin wake hudu  da ake kyatata zaton 'yan boko haram ne sun kai harin kunar bakin wake a wajen birnin Maiduguri na arewa maso gabashin Najeriya.

An kai harin ne a tashar motar Muna da ke kan hanyar Mafa-Dikwa,inda aka bayyana harin a matsayin mafi muni a jerin hare-haren da aka kai a cikin 'yan kwanakin nan cikin jihar ta  Borno.

Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da dake hare-haren a tashar motar ta Muna, da ke kusa da sansanin 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu.

A ranar Litinin da ta gabata ma, an kai wani hari a jahar ta Borno, da ya hallaka mutane 9.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky