Harin Boko Haram Ya Lashe Rayukan Jami'an Tsaron Najeriya 10

Harin Boko Haram Ya Lashe Rayukan Jami'an Tsaron Najeriya 10

Shugaban 'Yan sandar jihar Borno dake shiyar arewa maso gabashin Najeriya ya sanar da mutuwar jami'an tsaron kasar 10 sanadiyar harin kungiyar boko haram

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar Sin ya nakalto Damian Chukwu shugaban 'yan sandar jihar Borno a jiya Alhamis cikin wani taron manema labarai da ya kira a birnin Maiduguri na cewa kimanin jami'an 'yan sanya 4 da sojoji 6 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin kungiyar Boko haram a yankin Rann dake cikin jahar Borno.

 Chukwu ya kara da cewa jami'an 'yan sandar hudu da suka rasu, na daga cikin jami'an yaki da ta'addanci da suke tabbatar da doka da oda a jahar.

Shugaban 'yan sandar jihar ta Borno ya ce akwai sama da jami'an 'yan sanda 500 dake cikin jami'an kwantar da zaman lafiya da tsaro a jahar Borno dake ake kira da lafiya dole


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky