Gwamnatin Najeriya tana kuskure Na Cigaba Da Tsare Zakzaky 

Gwamnatin Najeriya tana kuskure Na Cigaba Da Tsare Zakzaky 

Gwamnatin Najeriya tana kuskure Na Cigaba Da Tsare Zakzaky  ~ Inji Buba Galadima:

Tsohon babban na hannun daman shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari kuma fitaccen dan adawar cikin gida Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa

cigaba da tsare jagoran 'yan shi'a a Najeriya sheik Ibrahim Zakzaky da gwamnatin tarayya ke cigaba dayi a matsayin kuskure da kuma rashin adalci tsagwaron sa.


Injiniya Buba Galadima ya bayyana hakan ne jiya a yayin da ake tattaunawa da shi a gidan talabijin din nan mai zaman kan sa na AIT a wani shiri da ake cewa "Focus Nigeria: Matters Arising"

A lokacin da aka tambaye shi ra'ayin sa game da cigaba da tsare jagoran na mabiya shi'a.


Daga karshe Injiniya Buba Galadima ya baiwa Gwamnatin kasar shawara da cewa tunda kotu ta yanke hukuncin sakin malamin to ya kamata Gwamnati ta cire Interest akan wannan Malamin.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky